Akwai Dalili: INEC Ta Yi Barazanar Soke Sakamakon Zaben Edo da Aka Dora a IReV


  • Hukumar INEC ta yi barazanar soke duk wani sakamakon zaben jihar Edo da aka dora a shafinta na IReV ma damar ya saba doka
  • INEC ta ce idan har ta gano cewa an tursasa jami’inta wajen ayyana sakamakon zaben, to ba makawa za ta yi amfani da karfin ikonta
  • Hakazalika, hukumar ta ce akwai matakan da aka tanada kan korafe-korafen da aka samu a yayin tattara sakamakon zaben jihar Edo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al’amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce tana da hurumin soke duk wani sakamakon zabe da aka ayyana ta hanyar tursasawa.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a safiyar Lahadi awanni bayan kammala kada kuri’a a zaben gwamnan jihar Edo.

See also  The Role of Technology in the Ehsaas Program

Kara karanta wannan

IREV: Ana daf da kammala daura kuri’un zaben Edo, an kusa sanin sabon gwamna

INEC ta yi magana kan soke sakamakon zaben jihar Edo
Edo: INEC ta bayyana dalilin da zai sa ta soke sakamakon zaben da aka dora a shafinta na IReV. Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter

Bayan ɗora sakamakon zaben da aka gudanar a shafin INEC na IReV, jam’iyyun siyasa daban-daban sun yi ta ikirarin samun nasara, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

INEC ta tattara sakamakon gundumomi

Amma a cikin sanarwar, Mohammed Haruna, kwamishina kuma dan kwamitin labarai da wayar da kan masu zabe ya ce hukumar na iya soke sakamakon da aka dora a IReV.

“Bayan kamma zabe a jiya, hukumar ta bude shafinta na IReV inda aka dora sakamakon zaben rumfuna. An kuma tattara sakamakon daga gundumomi 192 na jihar.

Haka zalika, an kammala tattara sakamakon zaben a mafi yawan kananana hukumomin jihar kuma jami’anmu na hanyar zuwa cibiyar tattara sakamakon da ke Benin City.”

INEC za ta iya soke sakamako

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Domin kauda shakku, za a fara tattara sakamakon zaben ne kamar yadda dokar zaben kasar ta 2022 ta tanadar. Akwai matakin da ake dauka kan korafe korafen tattara sakamako.

See also  Government of Pakistan has Announced New Budget Benazir Kafalat Program Payment

Kara karanta wannan

‘Dan acaba ya lashe kujera a APC da aka fadi sakamakon zaben kananan hukumomi

“Idan har muka tabbatar da cewa jami’inmu ya ayyana wani sakamakon zabe bisa tursasawa, to ba shakka hukumar za ta iya amfani da karfin ikonta ta soke wannan zaben.”

INEC ta kuma shaida cewa za a baiwa wakilan jam’iyyu da aka amince da su, masu sa ido da kuma kafafen yada labarai damar shiga cibiyoyin tattara sakamakon zaben.

Asali: Legit.ng





Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *