Edo 2024: Yadda APC Ta Lashe Zabe bayan Samun Nasara a Kananan Hukumomi 11
- Dan takarar jam’iyyar APC, Monday Okpebholo ya lashe zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar a ranar Asabar 21 ga watan Satumba
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana Okpebholo matsayin wanda ya lashe zaben bayan samun kuri’u 291,667
- Legit Hausa ta tattaro cewa jam’iyyar APC ta samu nasara a kananan hukumomi 11 yayin da mai bi mata, PDP ta samu lashe guda bakwai
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al’amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo – Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Edo.
A ranar Asabar, 21 ga watan Satumba ne aka gudanar da zaben inda INEC ta sanar da sakamakon a ranar Lahadi a birnin Benin.
Legit Hausa ta ruwaito cewa Monday Okpebholo ya lashe zaben Edo ne da kuri’u 291,667 bayan da ya samu nasara a kananan hukumomi 12 cikin 18 na jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Sakamakon zaben jihar Edo
Duk da cewa jam’iyyar PDP ce ke mulki a Edo, sai dai hakan bai hana al’umma zaben wanda suke ganin shi ne ya fi cancanta ya gaji Gwamna Godwin Obaseki ba.
Amma dai jam’iyyar PDP ta nuna rashin amincewarta kan wannan sakamako inda ta yi ikirarin cewa an tafka kurarai musamman a wajen tattara sakamako.
A jimillar kananan hukumomi 18 na Edo, APC ta samu kuri’u 291,667 yayin da PDP ta zo ta biyu da kuri’u 247,655 inda LP ke da kuri’u 22,763.
Kananan hukumomin da APC ta lashe
Ga jerin kananan hukumomin da dan takarar APC, Monday Okpebholo ya lashe a zaben, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
1. Esan ta Yamma
APC – 12,952
PDP – 11,004
LP – 342
2. Owan ta Yamma
APC – 12,277
PDP – 11,284
LP – 201
3. Karamar hukumar Egor
APC – 16,760
PDP – 14,658
LP – 1,966
4. Akoko Edo
APC – 34,847
PDP – 15,865
LP – 2,239
5. Esan ta tsakiya
APC – 10,990
PDP – 8,618
LP – 418
6. Karamar hukumar Orhionmwon
APC – 16,059
PDP – 14,614
APC – 556
7. Owan ta Gabas
APC – 19,380
PDP – 14,189
LP – 446
8. Etsako ta Gabas
APC – 20,167
PDP – 9,683
LP – 604
9. Etsako ta tsakiya
APC – 11,906
PDP – 8,455
LP – 381
10. Etsako ta Yamma
APC – 32,107
PDP – 17,483
LP – 2,116
11. Karamar hukumar Oredo
APC – 30,780
PDP – 24,938
LP – 5,389
Edo: PDP ta lashe kananan hukumomi 7
A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa jam’iyyar PDP ta samu nasarar lashe kananan hukumomi bakwai cikin 18 a zaben jihar Edo da aka gudanar.
Dan takarar PDP, Asu Ighodalo ya samu kuri’u 247,655 a dukkanin kananan hukumomin jihar yayin da Monday Okpebholo na APC ya lashe zaben da kuri’u 291,667.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng