Sakamakon Zaben Edo: Dan Takarar PDP, Ighodalo Ya Samu Nasara a Karamar Hukumarsa


  • Hukumar zabe ta INEC ta bayyana jam’iyyar PDP a matsayin wacce ta lashe karamar hukumar Ovia ta Arewa maso Gabas ta Edo
  • An rahoto cewa PDP ta samu kuri’u 14,199 inda ta doke jam’iyyar APC wadda ta samu kuri’u 8,398, yayin da Labour Party ta samu kuri’u 98
  • Har yanzu dai hukumar INEC na ci gaba da tattarawa tare da sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da aka yi jiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al’amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo – Dan takarar gwamnan jihar Edo a karkashin jam’iyyar PDP Asue Ighodalo ya yi nasara a karamar hukumarsa ta Esan ta Kudu maso Gabas.

An bayyana hakan ne a yayin tattara sakamakon zaben jihar da jami’in baturen zabe, Farfesa Faruq Adamu Kuta, mataimakin shugaban jami’ar FUT da ke Minna ya jagoranta.

See also  Punjab Government delivers electric and petrol bikes to students

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Ana jiran karamar hukuma 1, APC ta ba PDP tazarar kuri’u sama da 50,000

Dan takarar PDP, Asue Igdohalo ya lashe karamar hukumarsa
Zaben Edo: Dan takarar ya lashe zabe a karamar hukumarsa ta Esan ta Kudu maso Gabas. Hoto: @Aighodalo
Asali: Twitter

Ighodalo ya kawo karamar hukumarsa

PDP ta samu kuri’u 14,199 inda ta doke jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ta samu 8,398, yayin da Labour Party ta samu kuri’u 98, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Ga yadda sakamakon ya kasance:

Karamar hukumar Esan ta Kudu maso Gabas na da gundumomin zabe 10.

APC – 8,398

PDP – 14,199

LP – 98

Mutanen da suka yi rijista – 90,240

Masu zabe da aka tantance – 23,390

Halartattun kuri’u – 22,780

Lalatattun kuri’u – 356

Gaba daya kuri’un da aka kada – 23,136.

See also  Understanding the 8171 Ehsaas Web Portal: A Step-by-Step Guide

Duba wasu labarai kan zaben Edo:

Kara karanta wannan

Sakamakon zaben Edo: Gwamna ya sha kaye a karamar hukumarsa, APC ta yi nasara

EFCC ta cafke masu sayen kuri’u

A wani labarin, mun ruwaito cewa jami’an hukumar EFCC sun cafke wasu mutane uku bisa zargin suna sayen kuri’u a zaben gwamnan jihar Edo.

An rahoto cewa mutanen da ke a wajen sun nuna turjuya lokacin da EFCC za ta tafi da wadanda aka kaman da suka hada da maza biyu da mace daya.

Asali: Legit.ng





Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *