Sakamakon Zaben Edo: Jerin Kananan Hukumomin da Ighodalo na PDP Ya Lashe
- Bayan kammala bayyana sakamakon zaben jihar Edo da hukumar INEC ta yi, an gano cewa jam’iyyar PDP ta lashe kananan hukumomi bakwai
- Dan takarar PDP a zaben gwamnan Edo, Asue Ighodalo ya samu jimillar kuri’u 247,655 a dukkanin kananan hukumomin jihar 18
- Sai dai hukumar INEC ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben Edo da kuri’u 291,667
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al’amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo – Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kammala tattarawa tare da bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Edo.
A ranar Asabar, 21 ga watan Satumbar nan ne aka gudanar da zaben gwamnan jihar yayin da INEC ta ayyana wanda ya alashe zabena a ranar Lahadi.
Sakamakon zaben gwamnan Edo
Legit Hausa ta ruwaito cewa INEC ta ayyana Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben Edo, kuma shi ne zababben gwamnan jihar na gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
INEC ta tsaya kan matsayarta duk da cewa an samu zarge-zarge daga jam’iyyun adawa musamman PDP na kura-kurai a zaben da kuma kin amincewa da sakamako.
A jimillar kananan hukumomi 18 na Edo, APC ta samu kuri’u 291,667 yayin da PDP ta zo ta biyu da kuri’u 247,655 inda LP ke da kuri’u 22,763.
Kananan hukumomin da PDP ta lashe
Ga jerin kananan hukumomin da dan takarar PDP, Asue Ighodalo ya lashe a zaben, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
1. Karamar hukumar Igueben
PDP – 8,470
APC – 5,907
LP – 494
2. Karamar hukumar Uhunmwonde
PDP – 9,339
APC – 8,776
LP – 767
3. Ovia ta Arewa maso Gabas
PDP – 15,311
APC – 13,225
LP – 1,675
4. Esan ta Kudu maso Gabas
PDP – 14,199
APC – 8,398
LP – 98
5. Esan ta Arewa maso Gabas
PDP – 12,522
APC – 10,648
LP – 194
6. Ovia ta Kudu maso Yamma
PDP – 10,260
APC – 10,150
LP – 849
7. Karamar hukumar Ikpoba-Okha
PDP – 26,382
APC – 16,338
LP – 4,026
Duba wasu labarai a kan zaben Edo
Sakamakon zaben Edo: APC ta ba PDP tazarar sama da kuri’u 50,000
Zaben Edo: APC ta lashe kananan hukumomi 12, PDP ta tsira da 6
Gwamna Obaseki ya ba PDP kunya, APC ta lashe karamar hukumarsa
INEC ta yi barazanar soke zabe
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi barazanar soke zaben gwamnan jihar Edo da aka dora a shafinta na IReV.
INEC ta ce ma damar ta gano cewa an tursasa wani jami’inta ayyana sakamakon zabe, ta ce za ta yi amfani da karfin ikonta wajen soke zaben wannan rumfa ko mazaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng