“Za a Sharbi Romon Dimukuradiyya:” Zababben Gwamnan Edo Ya Yi Albishir
- Zababben gwamnan Edo, Monday Okpebhola ya dauki alkawarin cicciba jihar zuwa matakin da kowa zai yi alfahari
- Mista Okpebhola ya dauki alkawarin daukar tsarin mulki irin na tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomole
- Ya gode wa jama’ar da suka fito tare da ba shi kuri’a 291,667 wanda ya ba shi damar lallasa takwarorinsa da PDP da LP
A’isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al’amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Edo – Zababben gwamnan Edo, Monday Okpebholo ya dauki alkawarin daukaka jihar da zarar ya kama aiki a matsayin gwamna.
A zaben ranar Asabar da mazauna jihar su ka gudanar ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Mista Okpebholo a matsayin zababben gwamna da kuri’a 291,667.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Asue Ighodalo na jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 247,274, sai Olumide Akpata da jam’iyyar LP da ya tattaro kuri’a 22,761.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Edo 2024: Okpebholo zai cigaba da aikin Oshiomhole
A zantawarsa da manema labarai a yammacin Lahadi, zababben gwamnan Edo Monday Okpebholo ya dauki alkawarin dora wa daga inda tsohon gwamna Adams Oshiomole ya tsaya.
Ya kara da cewa zai kuma yi irin aikin da tsohon gwamnan Akwa Ibom, kuma shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya gudanar a zamanin ya na gwamna.
Zababben Gwamna Okpebholo ya godewa mutanen Edo
Monday Okpebholo, ya gode wa jama’ar da su ka yi tururuwar zabarsa a jihar Edo, tare da bayyana cewa ba su yi zaben tumin dare ba.
“Na yi murna sosai, kuma ina godiya ga jama’ar Edo da su ka zabi wanda a dace. Za a samar da Edo sabuwa,’ cewar Monday Okpebholo.
APC ta yi zarra a zaben Edo
A baya mun wallafa cewa jam’iyyar APC ta kan gaba a zaben Edo da ya gudana a ranar Asabar, inda bayan sanar da sakamako daga mazabu aka gano tazarar da ke tsakanin APC da PDP.
Bayan karanta sakamakon zaben gwamnan Edo daga kananan hukumomi 16, jam’iyyar APC ta shiga gaba inda ta samu kuri’a 275,329 yayin da PDP ke take mata baya da kuri’a 220,892.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng