Zaben Edo: INEC Ta Sanar da Lokacin Ci Gaba da Tattara Sakamako


  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi ƙarin haske kan tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo
  • Kwamishin INEC na jihar, Anugbun Omuoha, ya sanar da cewa za a ci gaba da tattara sakamakon zaɓen da misalin ƙarfe 10:00 a ranar Lahadi
  • Anugbum Omuoha ya ba ɗa tabbacin cewa za a gudanar da aikin tattara sakamakon zaɓen cikin gaskiya da adalci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al’amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo – Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da lokacin da za ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo.

Hukumar INEC ta bayyana cewa za ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnan da aka gudanar ranar Asabar da misalin ƙarfe 10:00 na safe a ranar Lahadi.

See also  Introduction Of An Online Procedure For Eligibility Check In Ehsaas Kafalat Program

Kara karanta wannan

Akwai dalili: INEC ta yi barazanar soke sakamakon zaben Edo da aka dora a IReV

INEC, Zaben Edo 2024
INEC za ta ci gaba da tattara sakamako da karfe 10:00 na safe
Hoto: INEC Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa an bayyana hakan ne a wata sanarwa da kwamishinan zaɓen INEC na jihar Edo, Dr Anugbum Omuoha ya fitar a safiyar ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]

Me INEC ta ce kan tattara sakamako?

Kwamishinan zaɓen ya tabbatarwa jama’a cewa za a gudanar da aikin tattara sakamakon zaɓen cikin gaskiya, daidai da ƙa’idojin hukumar, rahoton jaridar Tje Guardian ya tabbatar.

“Ana sanar da jama’a, masu ruwa da tsaki, da masu sa ido cewa za a ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo da ke gudana a yau Lahadi, 22 ga watan Satumba, 2024, da misalin ƙarfe 10:00 na safe.”

“Mun yaba da haƙuri da haɗin kan da jam’iyyu suka bamu yayin da muke ƙoƙarin tabbatar da sahihin sakamako mai inganci na wannan muhimmin zaɓe.”

– Anugbum Omuoha

See also  Required Documents for Apni Chhat Apna Ghar Complete Details For 15 Lakh Loan

Anugbum Omuoha ya ƙara da yin kira ga masu ruwa da tsaki da su kwantar da hankulansu, inda ya jaddada cewa INEC ta jajirce wajen ganin an gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci a jihar Edo.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: ‘Yan sanda sun dauki mataki bayan gwamna ya dira a ofishin INEC

Ƴan sanda sun kori Obaseki daga ofishin INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa DIG Frank Mba ya tilastawa Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo fita daga harabar ofishin hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) da ke Benin.

Gwamna Obaseki dai yaje harabar ne da daddare misalin ƙarfe 2:00 na dare kuma yana nan har sai da ƴan sanda suka yi masa rakiya zuwa waje.

Asali: Legit.ng

See also  Community Participation in the Ehsaas Program





Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *