Zaben Edo: INEC Ta Soma Fadin Sakamako, PDP Ta Shiga Gaban APC da Kuri’u 8470
- Jam’iyyar PDP ta samu nasara a karamar hukumar Igueben yayin da hukumar INEC ta soma fadin sakamakon zaben jihar Edo
- An rahoto cewa jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 8, 470 yayin da APC ke binta a baya da kuri’u 5,907 da kuma LP mai kuri’u 494
- A ranar Asabar, 21 ga watan Satumbar 2024 ne al’ummar jihar Edo suka fita kwansu da kwarkatarsu domin zaben sabon gwamna
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al’amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo – Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kaddamar da fara tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da aka gudanar a jiya Asabar.
Hukumar ta fara soma fadin sakamakon zaben karamar hukumar Igueben inda jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 8470 wanda ya ba ta nasara kan sauran jam’iyyu.
PDP ta lallasa APC a Igueben
Rahoton Channels TV ya nuna cewa APC ta samu kuri’u 5,907 yayin da jam’iyyar Labour ta samu kuri’u 494.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Ga yadda sakamakon ya kasance:
APC – 5,907
PDP- 8,470
LP – 494
Mutanen da suka yi rijista – 54,549
Wadanda aka tantance – 15,274
Kuri’un da aka kada – 15, 267
Kuri’un da aka amince da su – 14,989
Lalatattun kuri’u – 278
An bayyana cewa wannan ita ce karamar hukumar farko da hukumar INEC ta bude fadin sakamakon zaben jihar Edo da ita.
Duba labarai kan zaben Edo:
INEC ta yi barazanar soke zabe
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar zabe ta kasa (INEC) ta yi barazanar soke duk wani sakamakon zaben jihar Edo da aka dora a shafinta na IReV ma damar ya saba doka.
INEC ta ce idan har ta gano cewa an tursasa jami’inta wajen ayyana sakamakon zaben, to ba makawa za ta yi amfani da karfin ikonta na soke sakamakon zaben.
Asali: Legit.ng