Zaben Edo: INEC Ta Yi Magana kan Dora Sakamakon Zabe a Na’urar IReV
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ƙasa (INEC) ta bayyana shirinta kan zaɓen gwamnan jihar Edo na ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024
- Kwamishinan INEC na jihar Edo ya bayyana cewa za a yi amfani da na’urorin BVAS wajen tantance masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen
- Anugbum Onuoha ya tabbatar da cewa za a ɗora sakamakon zaɓen a kan na’urar IReV idan ba a samu matsalar sabis ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al’amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta yi ƙarin haske kan hanyar tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Edo.
Hukumar INEC ta bayyana cewa za a tattara sakamakon zaɓen ta hanyar yin amfani da na’urar BVAS.
INEC za ta ɗora sakamako a IReV
Kwamishinan hukumar INEC na jihar Edo, Anugbum Onuoha ya bayyana hakan yayin tattaunawa da tashar Arise tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a [email protected]
Kwamishinan na INEC ya bayyana cewa bayan kammala tattara sakamakon zaɓen za a ɗora a IReV idan har ba a samu matsalar sabis ba.
“Muna da rumfunan zaɓe 4,519 a cikin ƙananan hukumomi 18. Ya zuwa yanzu mun aika da na’urorin BVAS guda 4,622 a ƙananan hukumomin.”
“Muna da ragowar guda 660 domin shirin ko ta kwana. Mun horar da jami’an da za su yi aiki da na’urar BVAS kuma sun shirya tsaf.”
“BVAS za ta tantance masu kaɗa ƙuri’a domin sanin adadin masu kaɗa ƙuri’a a kowace rumfar zaɓe. Za mu gudanar da zaɓen da za mu yi alfahari da shi.”
“Bayan kammala kaɗa ƙuri’a, za a ƙirga yawan ƙuri’un da aka samu sannan za a ɗora su a IReV idan a wajen babu matsalar sabis.”
– Anugbam Onuoha
Zaɓen Edo: Jigon APC ya yi hasashe
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigon jam’iyyar APC, Francis Okoye, ya yi hasashen wanda zai lashe zaɓen gwamnan jihar Edo wanda za a gudanar a ranar Asabar, 21 ga watan Satumba.
Francis Okoye ya ce babu makawa ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Sanata Monday Okpebholo, zai kayar da ɗan takarar jam’iyyar PDP, Asue Ighodalo.
Asali: Legit.ng